BINKICE; Masana a Amurka sun gano yin azumi sau 2 a mako na kara tsawon rai da riga-kafin cututtuka

BINKICE; Masana a Amurka sun gano yin azumi sau 2 a mako na kara tsawon rai da riga-kafin cututtuka

 

Malaman Kimiyyar Amurka sun bayyana cewar sakamakon wani bincike da suka gudanar ya bayyana yin azumi a kowanne mako ko kuma kame baki daga barin cin abinci na wasu awanni a rana na kara tsawon rayuwa tare da riga-kafin cututtuka da dama.

 

Sakamakon binciken da aka buga a mujallar Likitanci ta New England ya ce cin abinci a cikin awanni 6 zuwa 8 sannan a kame a awanni 16 zuwa 18 na kowacce rana na kara tsawon rai, rage karfin harbawar jini da riga-lafin cututtuka da dama.

 

Rahotonnin da muka samu daga jaridar TRT ya ce yin azumi a kwanaki 2 a kowanne mako na iya maganin cututtukan zuciya, kiba da ciwon sukari a saboda haka ake shawartar mutane da su yi hakan.

 

Binciken da aka gudanar a kan mutane da dabbobi ya nuna yin azumin na daidaita yanayin sarrafuwar abinci da gudanar jini a jikin dan adam, sannan yana sabunta lafiya.

 

Haka zalika na magance kwayoyin Insulin na jikin mutum wanda hakan abu ne mai kyau ga masu ciwon sukari.

 

Dabo Fm

Leave a Reply

Your email address will not be published.