Maryam Hiyana Ta Sami Nana Khadijat A Haihuwarta Karo Na Biyar

TSOHUWAR jaruma Maryam Usman (Hiyana) ta ƙara samun haihuwa inda a wannan karon Allah ya azurta ta da samun ‘ya mace.

Hajiya Maryam ta haihu ne a ranar Juma’a, 13 ga Disamba, 2019.

A ranar sunan, an saka wa jaririyar suna Nana Khadija.

An yi shagalin bikin sunan a gidan mijin Maryam da ke Kano.

‘Yan fim mata da dama sun halarci wajen, cikin su akwai Fauziyya Sani (Maikyau) Samira Ahmad, Ruƙayya Dawayya, da sauran su.

Wannan ita ce haihuwa ta biyar da Hiyana ta yi bayan ta yi aure. Yanzu ta na da maza uku, mata biyu.

Da fatan Allah ya raya su, ya sa masu jinƙan iyaye ne.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.