Yan Bindiga Dadi Sunyi Awun Gaba Da Miji Da Matarsa A yankin Katsina

 

 

Daga Yahaya Muhammad, Abuja

 

A daren jiya ne wasu ‘yan bindiga suka sace wani Alhaji Kanti da matarsa ​​Hajiya Zabi a gidansu da ke kusa da kauyen Kagara a karamar hukumar Dutsinma.

 

Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun afka wa gidansa da misalin karfe 2 na dare kuma sun kwashe su sun tafi dasu har zuwa wani wurin da ba a san inda suke ba.

 

Daga baya ‘yan bindigar sun farma kauyen Karofi kuma a yayin da suka yi fashi, sai dai jami’an tsaro sunyi Nasarar tarwatsa su.

 

Rahotanni sun kuma nuna cewa su dira kauyen Zabuwa a karamar hukumar Safana yayin da suka yi awun gaba da shanu 20 da tumaki 7.

 

Har yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta amsa tambayoyin binciken da aka yi kan lamarin ba.

 

Idan za a iya tunawa wannan harin ba zato ba tsammani ya zo kwana biyar bayan makamancin wannan a gidan shamsuddeen Yusuf da ke makarantar Kwata sakandare ta Dutsinma yayin da suka tafi tare da matar sa Nana Bilkisu, da kanwarta Aisha. Aliyu da diyarsa Afnan Shamsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.