PRE-WEDDING PICTURES KO FITO-NA-FITO DA ALLAH!

Daga Jamilu Sama’ila Dandana

Wannan dabi’a ta yin hotuna kafin aure da wasu matasanmu suka kwaikwayo daga Turawa Wanda ake Kira pre-wedding picture, Wadda ke basu damar yin shegantakarsu yayi hannun Riga da kowane addini.

A wurinne suke samun damar yin daukekeniya da Kuma rungumemeniya da sunan wayewa ko nunawa duniya wai su masoya ne!

Babu shakka dukkan soyayyar gaskiya na tafiya kafada da kafada da kishi, duk Wanda kaga kuwa ya dau hotunnan har ya baza su ga duniya to babu shakka baya kishin iyalinsa.

Yadda su masoyan ke caje juna kafin aurensu Wanda hakan K’arara haramun ne domin kuwa bata zama Mallakinsa ba.

Yin irin wadannan hotuna Kuwa kamar tallatawa kwartaye matar ka ce, domin kuwa ganin hotunan zai saukaka musu neman wurin aikewar su.

Ya kamata iyaye su sani wallahi dukkan abunda kaje yazo tofa suma akwai nasu kason na zunubi.

Sannan yan uwa mata ku daina Bari soyayya na zama linzamin tafiyar da rayuwarku domin kuwa ku sani kamar zuga ce kuke yiwa yayanku masu zuwa.

Dole ne samari mu saka addini a gaba fiye da kowane sabon abu yazo mana, matukar muna son ganin daidai.

One thought on “PRE-WEDDING PICTURES KO FITO-NA-FITO DA ALLAH!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: