Ku Bada Gudunmawa Wajen Samar Da Tsaro A Najeriya – Buhari Ga Sabbin Jami’an ‘Yan Sanda

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaye daliban kwalejin horon ‘yan sanda dake Wudil, jihar Kano a ranar Alhamis, 19 ga Disamba, 2019.

 

A bikin yaye daliban 628, Buhari ya yi kira ga jami’an hukumar ‘yan sanda su kasance masu gaskiya da kwarewa wajen aiki saboda yardar da ‘yan Najeriya sukayi da su.

 

Buhari wanda ya kasance bako na musamman, ya yi kira da jamian ‘yan sandan su jajirce wajen kawar da rashin tsaro a jihar.

 

Shugaban kasan ya tabbatarwa ‘yan sandan cewa gwamnatinsa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.

 

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Dingyadi, da sarakunan jihar Kano biyar, da sauran manyan baƙi a ciki da wajen jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: