Kiran Tsige Sanusi: Ƙarya Ganduje Ya Yi Mana – Ƙungiyoyi

Gamayyar Kungiyoyin kishin al’ummar Kano ta Civil Society Forum sun musanta cewa sun aikewa fadar gwamnatin Kano bukatar a tsige sarki Muhammadu Sanusi na biyu daga mukaminsa.

 

Wannan na kunshe a wata wasika da kungiyoyin suka aikewa fadar gwamnatin Kano, suna masu cewa kungiyoyin Civil Society Organisation basu aike da wasikar bukatar a sauke Muhammadu Sanusi na biyu daga karagar mulki ba, bada yawunsu aka yi hakan ba.

 

Kano Civil Forum dai ta kira waccan kungiyar da ta bukaci a sauke sarkin Kano daga mukaminsa a matsayin kungiya ta bogi.Kungiyar dai a cikin wasikar da ta aikewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana masa cewa akwai kungiyoyi masu zaman kansu sama da 183 da ke karkashinta da suka mayar da hankali wajen kare hakkin jama’a, harkokin kiwon lafiya, ayyukan raya kasa, harkokin tsaro da zaman lafiya.

 

Kano Civil Forum ta ta kuma yi Allah wadai da yadda wasu daidaiku ke amfani da siyasa wajen tayar da zaune tsaye, ta yadda suke fakewa da wata kungiya mai zaman kanta ta bogi.Muna mai nesanta kanmu daga wasikar da aka aikewa mai girma gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ke neman a tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu daga kan mukaminsa”, a cewar kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *