Idan Na Fallasa Abinda Ke Faruwa A Najeriya, Babu Wanda Zai Iya Barci – Danjuma

Tsohon ministan tsaro, Janar TY Danjuma, ya ce idan ya fallasa abubuwan da ke faruwa a kasar nan, yan Najeriya ba zasu iya bacci ba.

 

Tsohon Sojan ya bayyana hakan a wani taron karrama wasu da lambar yabo da kaddamar da littafi kan shekaru 70 da aikin jarida na jaridar Tribune, da ya gudana a jami’ar Ibadan, jihar Oyo.

 

Yace: “A kasar Yarabawa, kowa ya zama zabo, matsorata. Kuma da alamun mutane basu damu da abinda ke faruwa ba. Idan na fada muku abinda ke faruwa a Najeriya a yau, ba zaku iya bacci ba.

 

“Muna cikin halin dar-dar a kasar nan. Kuma mutanen da suka sanyamu cikin wannan hali sun cigaba a yau. Saboda haka ya kamata mu tashi tsaye. Shine hanya daya na tsirar da kawunanmu.”

 

“Abubuwan da Yan jaridar bogi keyi ba ya taimakonmu. Muna rokon Ubangiji ya cigaba yiwa kasar nan albarka, amma mu kadai zamu iya ceton kanmu.”

 

Allah Ya kawowa Mana karshen Wannan masifa Amiin

Leave a Reply

Your email address will not be published.