Kotu Ta Daure Wani Matashi Daurin Rai Da Rai A Jihar Jigawa Bisa Laifin Fyade

Babbar kotin jiha Jigawa mai lamba ta biyu dake zaman ta a Dutse ta daure wani mai suna Yakubu Muhammad daurin rai da rai bisa laifin aikata fyade.

Mutumin dan shekaru 40 dake zaune a unguwar Kachi dake Dutse an same shi da lefin kai ‘yan mata biyu gidansa a 2017 inda ya yi lalata da su bayan ya ba su naira dari dari kowaccensu.

Da yake zartar da hukunci, alkalin kotin mai shari’a Ahmed Isa Gumel ya ce hukuncin zai kasance izina ga masu aikata fyade a jihar nan kasancewar aikata fyade yayi kamari a jihar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: