Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sunan Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan zuwa ga majalisa domin tantance shi a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta kasa.
Ustaz Zikirullah, wanda dan asalin jihar Osun ne, zai maye gurbin Muhammad Mukthar ne a matsayin shugaban hukumar ta Alhazai bayan wa’adin sa ya cika.