Ɗiyar Shugaba Buhari Ta Kammala Karatun Digirin Farko A Landan 

Hanan Muhammadu Buhari

Ɗiyar Shugaba Buhari Ta Kammala Karatun Digirin Farko A Landan

 

Ɗiyar shugaba Muhammadu Buhari, A’isha Buhari wacce aka fi sani da laƙabin suna (Hanan), ta samu nasarar kammala digirinta na farko a Jami’ar birnin Landan.

 

An gudanar da bikin yaye su a wannan rana ta Talata, bikin da ya samu hakartar Mamarta, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari da sauran ƴan’uwanta.

 

Hanan ta gudanar da aikin rubuta kundinta (Project) na kammala karatun digirin a Jihar Kebbin Nageriya, sannan kuma ta samu nasarar fita daga jami’ar da gagarumin sakamako mai daraja ta ɗaya (First Class).

 

Hanan ta kasance ɗaliba mai matuƙar ƙoƙari da hazaƙa inda ta ke da sha’awa da kuma ƙwarewa kan ɗaukan Hoto da sauran ayyukan fasaha na zane-zane da ƙirƙire-ƙirƙire.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.