An Yanke Masa Hukuncin Wata Shida A Gidan Yari, Bayan Ya Saci Waya A Masallaci A Garin Zaria

 

kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Tudun Wada Zaria ta yanke wa wani matashi mai suna Mohammed Abdullahi hukuncin zaman gidan kaso na tsawon watanni shida bayan ya saci wayar salula ta naira dubu 10,000 a Masallaci.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, dan sanda mai shigar da kara, Sajan Adamu Yahaya ya bayyanawa kotu cewa barawon ya kutsa kai cikin wani Masallaci dake filin Mallawa, Tudun Wada Zaria da sunan zai yi sallah, amma sai ya sace wayar wani mutumi da kudinta ya kai naira dubu 10,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published.