‘Ya’yana Guda Saba’in Ne Suka Haddace Kur’ani, Cewar Sheik Dahiru Bauchi

…ku karanta takaitaccen tarihin Shehin Malamin

Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin darikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al’kur’ani, littafin musulmi mafi girma.

Shehun malamin na daya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Tarihin sheikh Dahiru Bauchi

Wannan tambaya ce da muka samu daga dumbin mutane da suka hada da Ahmad Muhammad da Wada Muhammad Musa Danmaliki Kumbotso Kano

BBC ta mika wannan tambaya ga Sheikh Dahiru Bauchi ga kuma amsar da ya bayar:

An haifi Sheikh Dahiru ne a ranar 28 ga watan Yunin 1927, dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346.

An haife shi a wani gari da ake kira Nafada da ke jihar Gombe, wanda garin mahaifiyarsa ce, “kasancewar a al’adar Fulani ana haihuwar dan fari ne a gidansu mahaifiyarsa,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Ni Bafulatani ne ta wurin uwa da uba. Dukkanin kakannina hudu Fulani ne.

“Sunan mahaifiyata Maryam ‘yar Hardo Sulaiman. Sunan Mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam.”

Sheikh Dahiru ya haddace kur’ani a wurin mahaifinsa kafin daga bisani ya tura shi Bauchi domin neman tilawa.

Mahaifinsa almajirin Shehu Ibrahim Nyass ne kuma mukaddami a cikin darikar Tijjaniyya ta hanyar Amadu Futiy kafin Shehi Ibrahim Nyass ya bayyana.

“Mahaifiyata ita ma ta je Kaulaha har sau biyu, kuma Shehu ya kaddamar da ita har ya ba ta carbi, saboda haka ni da mahaifina da mahaifiyata da ‘ya’yana da jikokina duk gaba daya mun taru a cikin Shehu Ibrahim,”

Ya yi auren fari a shekarar 1948 lokacin yana da shekara 20 “da wata daya.”

Yawan ‘ya’yan Shehu
Tambaya ce da muka samu daga Murtala Shu’aibu Gama

Sheikh Dahiru ya ce yana da ‘ya’ya kimanin 80 kuma 70 daga cikinsu sun haddace alkur’ani.

“Wasu daga cikin yarana sun haddace kur’ani tun suna shekara bakwai da haihuwa kuma tun ma kafin su iya rubutu a allo.

“Akwai yarana hudu da suka haddace kur’ani a shekara biyar kamar daya daga cikin ‘ya’yana da ke Kaduna. Su da ka suke haddacewa amma dai ba zai hana su rubutu a allo ba idan suka girma.

“Sai dai ban sani ba ko a cikin ‘ya’yan nawa akwai wanda ya rubuta kur’ani saboda su kan fita kasashen waje domin neman karatu na sauran fannonin addini da ma boko.

“Yanzu ma akwai daktoci a cikin yaran,” a cewar Shehun Malamin.

Matan Shehi nawa?

Mun sami wannan tambayar ne daga Usman Sale Jimeta da Salisu Garba Warure.

BBC kuma ta mika tambayar ga daya daga cikin ‘ya’yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya bayar da amsa kamar haka:

“Matan Shehi hudu ne a yanzu haka. Sai dai kuma da dama sun mutu sannan kuma wasu da dama sun fita.”

A ina ya Shehi ya yi karatu?

Tambaya ce da muka samu daga mutane da dama amma da yawansu ba su fadi sunayensu ba.

Sheikh Dahiru ya ce ya haddace kur’ani a hannun mahaifinsa Alhaji Usman dan Alhaji Adam ne domin shi ma mahaddacin alkur’ani ne.

Daga nan ne ya tura shi wurin malamai da dama domin tilawa, “kuma Alhamdulillahi na kan ji mutane na karin gishiri suna kira na gwani,” in ji Malam.

Malam ya je Bauchi domin karatu. Malaman da ya yi karatu a hannunsu sun hada da Malam Ahmadu na Sabon gari da Gwani dan Fika da malam Alhaji na Gombe da dai sauran su.

Ya kara da cewa: “Ba gaskiya ba ne cewa na yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara. Malam Abubakar Gumi ne ya yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara.

“Na kuma karbi darikar Tijjaniya a hannun mahaifina.

Daga BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published.