MASARAUTUN KANO; Gwamnatin jiha tana sake duba hukuncin da kotu ta yanke.

Gwmanatin jihar Kano tace tana sake duba hukuncin da kotu ta yanke kan kirkiro da masarautun domin daukan matakin da ya dace cikin gaggawa.

Sanarwa dake dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, tayi nuni da cewa duk da ikon da dokar kasa ta baiwa majalisar dokokin jihar na kirkiro da masarautun bisa la’akari da amfanin yin hakan yake dashi, kotu ta yanke hukuncin da bai dace ba.

Don haka sanarwar tace Gwamnatin jihar ba zata nade hannu ta zuba ido akan lamarin ba, wanda hakan ya take Ikon da majalisar ke da shi na yiwa al’umma abin da suke muradi.

Duk da hukuncin, Gwamnatin jihar Kano har yanzu tana kallon wadannan masarautun a matsayin masarautu masu matsayi na matakin farko kuma zata ci gaba da aiki da su.

Don haka Gwamnatin jihar Kano take jan hankalin jama’a su kasance masu bin doka da oda tare da jiran abin da Gwamnati zata yi kan hakan nan Ba da Jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.