Shari’ar Musulunci Ba Ta Yarda Da Auren Dole Ba – Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria

Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria

Shari’ar Musulunci Ba Ta Yarda Da Auren Dole Ba – Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria

 

Shari’ar musulunci ba ta yarda da auren dole ba, babu wata mazhaba da ta yarda da auren dole sai mazhabar Imamu Malik, shi ma Imamu Malik bai dogara da wani nassi ba, sai dai yana ganin karfin uba da hankalinsa da natsuwarsa fiye da na diyarsa, saboda haka yake ganin shi yafi dacewa ya zaba mata miji saboda ita tana da karancin hankali, da karancin fahimta, amma wannan hukuncin mazhabar malikiya kadai ta zo da shi, a sauran mazhabobi babu auren dole. shiyasa maulanmu Shehu Ibrahim Inyass yace, da Imamu malik na raye da na kalubalance shi akan wannan maganar na auren dole, saboda ni ban ga maganar auren dole a sunnar manzon Allah SAW ba.

 

Malamai sun ce, idan mace ta zabi wanda take so ta aura, waliyinta (mahaifinta) ma ya zabo wani daban wanda yake so ya aura mata, idan dai wanda ta kawo kuf’in ta ne, ma’ana, musulmi ne kamamme wanda zai iya rike ta, to wanda ta zaba yafi cancanta a aura mata, ko da wanda waliyinta ya zaba shima kuf’i (musulmi kamamme) ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published.