Yadda Jonathan Ya Hana Mu Ceto ‘Yan Matan Chibok, Cewar Firaministan Burtaniya

 

…Kasashen Amurka Da Burtaniya Sun So Wulakanta Ni Saboda Na Ki Amincewa Da Auren Jinsi, Cewar Jonathan

 

Daga Rilwanu Labashu Yayari

 

Tsohon shugaban Nijeriya, Dakta Goodluck Jonathan, ya bayyana wani boyayyen shirri mai cike da ban mamaki.

 

Hakan na na zuwa ne bayan da yake mayarwa tsohon Fira Ministan Birtaniya, David Cameron, martani akan wata tuhuma da ya yi wa Jonathan.

 

Jaridar Dabo FM ta binciko cewa; Cameron ya soki shugaba Jonathan, a wani littafi daya wallafa mai sunan ‘For The Record’, inda ya bayyana Dr Jonathan a matsayin wanda ya ki amincewa da bukatar shi (David Cameron) akan taimaka wa Nijeriya don ceton rayukan ‘yan matan Chibok.

 

Da yake mayar da martani, Jonathan ya fallasa cewa, kasar Amurka da Birtaniya tare da abokan hamayyar shi sun zauna don bullo da hanyar wulakanta shi akan ya yi watsi da bukatar turawa ta yin auren Jinshi a Nijeriya.

 

Ga wasu daga cikin martanin tsohon shugaban Kasar.

 

“Martani na ga ikirarin David Cameron

 

Na karanta kalaman tsohon Fira Ministan Burtaniya, David Cameron, a cikin sabon littafinsa, mai suna ‘For The Record, wanda ya zarge ni da Gwamnatin Najeriya wacce na na jagoranta, zargin cin hanci da rashawa da kuma kin amincewa da taimakon da Gwamnatin Biritaniya taso bawa Najeriya wajen kubutar da ‘yan matan Chibok da aka sace ranar 14 Afrilu, 2014.

 

Abin bakin ciki ne ace Mista Cameron zai faɗi wannan saboda babu abin da ya taɓa faruwa duk cikin abinda ya fada.

 

A matsayina na Shugaban Najeriya, ban rubuta wasika ga FiraMinista David Cameron kadai ba, na rubuta wa Shugaban Amurka na wancan lokacin, Barrack Obama, da Shugaban kasar Faransa na wancan lokacin, François Hollande, da Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na rubuta ina kirasu dasu taimaka wajen ceto ‘Yan Matan na Chibok.

 

Ta yaya ni da na mika bukatar taimako, ance za’a taimaka kuma ince banaso?

 

Tarihi ma ya musanta maganar Mr. Cameron.

 

A ranar 8 ga Maris, 2012, lokacin da kungiyar Boko Haram sukayi garkuwa da wani dan asalin kasar Ingila mai suna Chris McManus, tare da wani dan kasar Italiya Franco Lamolinara, a Sakkwato. A matsayina na Shugaban Najeriya, da kaina na baya gamawayyar wasu Sojojin Birtani tare da gamayyar jami’an tsaron Najeriya na musamman, izini don ayi kokarin ceto mutanen da aka dauke.

 

Saboda haka ni da nayi wannan hubbasar, mai zai sa idan da an bukaci a bamu taimakon ceto ‘Yan Matan Chibok zance, Bamaso?

 

Haka kuma ya zargeni da saka siyasar kabilanci a wajen nada shuwagabannin tsaro.

 

Ban kasance mai rufe da ido tare da nuna kabilanci ba, a cikin wadanda na bawa mukamai, dayawa bamu taba haduwa dasu ba, na nada sune gwargwadon tarihin kwarancewar aikinsu.

 

Duk ni dan kudu ne, yawanci shuwagabannin tsaro da na nada duk yan Arewa ne.

 

Ni dai, na san cewa Mr. Cameron ya dade yana jin haushin na kan dalilan dayawa.

 

A ranar 24 ga Yuli, 2013, yayin bikin murnar dokar halatta Auren Jinsi a 2013, Mr. Cameron ya ce “Ina son fitarwa da duniya auren Jinsi”.

 

A yayin wannan taron, ya yi tunkawon cewa zai tura mutane zuwa kasashe don tabbatar da auren Jinsi a ciki har da Najeriya.

 

Na sha matsin lamba daga gwamnatin Cameron, akan sai na rattaba hannu don halarta auren Jinsi. Sai dai baisani ba a matsayina na shugaban Najeriya, na rantse da littafin Bible cewa bazanyi wani abin da ya sabawa yan Najeriya ba.

 

Don haka, a ranar Litinin, 13 ga Janairu, 2014, Na sanya hannu kan dokar hana auren jinsi guda-daya, dokar da ta samu goyon baya da rinjaye a Majalissar dokokin Najeriya.

 

Hakan ya zo ne jim kadan bayan da wata cibiyar kidudduga a Amurka ta fitar da rahoto cewa kaso 98 na mutanen Najeriya basa ra’ayin auren Jinsi.

 

Nan da nan bayan da na ɗauki wannan matakin na kishin ƙasa, gwamnati na ta sami matsin lamba mai ƙarfin gaske daga Mista Cameron, wanda ya kai yayi ta turomin sakonni.

 

A zahiri, an gudanar da taruka a Fadar White House ta Obama da kuma a Portcullis House da ke Majalisar Dokokin Birtaniya, tare da abokan hamayya ta domin a wulakanta ni kan na sanya hannu don haramta auren Jinsi.

 

Dr. Goodluck Jonathan, Shugaban Gidauniyar Goodluck Jonathan kuma Shugaban Najeriya 2010-2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published.