Ko Ƙauracewa Fadar Shugaban Kasa Da Aisha Ta Yi Na Da Alaƙa Da Zargin Zawarcin Da Buhari Ke Yi Wa Sadiya?

NAZARI

Ko Ƙauracewa Fadar Shugaban Kasa Da Aisha Ta Yi Na Da Alaƙa Da Zargin Zawarcin Da Buhari Ke Yi Wa Sadiya?

 

A halin da ake ciki yanzu dai wani abu da ya ɗauki hankalin jama’ar Najeriya shine yajin da uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi daga fadar shugaban ƙasa, da kuma zargin neman Minista Sadiya Faruq da ake wa Buhari.

Sadiya Faruq ‘yar asalin jihar Zamfara, bincike ya nuna cewa da akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninta da mai girma shugaban ƙasa Buhari tun da daɗewa, rahotanni sun nuna cewar ta daɗe a tafiyar Buhari tun zamanin da ya yi takara a Shekarar 2011 lokacin Jam’iyyar CPC.

Tun a wancan lokaci jama’a suka fahimci da akwai soyayya da ƙaunar juna a tsakanin su da Buhari, amma zargi ne kawai saboda a wancan lokacin Sadiya Faruq tana da Miji, amma hasashen jama’a akan alaƙar Buhari da ita ya sake fitowa fili a wannan karon bayan mutuwar auren ta.

A zaɓen ministoci da Buhari ya yi ya zaɓo Sadiya daga Zamfara, kuma daɗin daɗawa shugaban ya ƙara bata shugabancin wata hukuma ta taimakawa ‘yan ƙasa da jarin kasuwanci wato (SPI) a taƙaice.

Amma a magana ta gaskiya dukkanin hasashen da jama’a ke yi na soyayya tsakanin Buhari da Minista Sadiya hasashen ne kawai, hakanan zargin da ake yi na cewar dalilin zargin neman da Buhari yake yi mata ne ya sanya uwargida Aisha Buhari barin fadar gwamnati na tsawon watanni, duka zargi ne wanda babu tabbas, domin tuni fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata cewa Aisha ta yi Yajin.

Sai dai kamar yadda aka sani shine, idan kaji gangami to da labari, kuma idan har babu Rami to mai ya kawo maganar Rami?

Leave a Reply

Your email address will not be published.