Shehu Aljan, Ya Kwato Shanu 430, Karkashin Kwamitin Da Gwamna Ganduje Ya Kafa A Jihar Kano

 

Gwamnatin jihar Kano ta nada kwamitin dawo da shanu da aka sace wanda wani attajiri mai suna Alhaji Shehu Aljan ya kwato.

Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Ganduje ne ya nada kwamitin Bisa Jagorancin Tsohon kwamishinan Ma’aikatar lura da kananan hukumomi, Commander murtala Sule Garo.

Da Tsohon kwamishinan Ma’aikatar Shari’a Barista Ibrahim Mukhtar a Matsayin Mataimakin Shugaba inda kuma Sauran Membobin suka hada da wakilan ‘yan sanda, Jami’an tsaro na farin kaya, Civil Defence, Miyetti Allah, Ma’aikatar kudade, da ta yada labarai da dai sauransu.

Tuni ma har kwamitin ya soma aiki inda ya gano shanun da aka sace kimanin 430 sa’annan kuma ya mika su ga masu shi.

Yayin da ake cigaba da binciken masu Dabbobin an samu mutane 17 wanda da gaske ne an sace musu dabbobi.

Shugaban kwamitin a jawabin sa ya godewa Gwamna Ganduje kan damar da ya bashi tare da bada tabbacin cewa za’a mikawa ainihin masu dabbobin idan har sun bayyana kansu.

Yace zai yi aiki tukuru domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.

Daga karshe ya kirayi wadan da aka sacewa dabbobin da su je kwanar Dangora dake karamar hukumar Kiru ta Jihar Kano domin a tantancesu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.