Ku Rubuta Ku Ajiye Sai Ya Sake Tsayawa Takara -Buba Galadima

 

Tun a farko dai dama wasu ‘yan Najeriya ne karkashin kungiyar dake goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya suka bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya gyara ta yadda shugaban kasar zai samu damar zarcewa a karo na uku.

Duk da dai fadar shugaban kasar ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ta musanta hakan, inda take cewa shugaban kasar ba shi da ra’ayin tsayawa takara a karo na uku.

Cikakken dan adawar ga shugaban kasar, Buba Galadima ya ce kwata-kwata wannan magana ta fadar shugaban kasa bai aminta da ita ba, inda ya bayyana cewa ba sau daya ba ba sau biyu ba gwamnatin shugaba Buhari ta sha yin amai ta lashe akan wasu abubuwa masu yawan gaske da suka gabata a kasar nan.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.