Manyan Dalilai Biyu Da Ya Sa Aka Rufe Boda, Inji Shugaban Kwastan, Hameed Ali

 

Gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta ne domin dalilan tsaro da kuma na tattalin arziki, a cewar shugaban hukumar kwastam na Najeriya, Hameed Ali.

Da yake magana da masu ruwa da tsaki da wakilan hukumomin tsaro a Seme dake jihar Legas, Ali ya ce gwamnati ba ta rufe iyakokinta domin muzguna kowa ba, tare da bayyana cewa ta yi hakan ne domin kishin kasa.

“Mu burin mu shine ganin cewa kasa ta samu tsaro, rayuwar jama’a ta inganta, sannan tattalin arzikin kasa ya bunkasa.

“An dauki matakin rufe iyakokin ne saboda kishin Nijeriya, ba a dauki matakin domin muzguna wa wani ba, sai don kare mutuncin kasar mu ,” a cewarsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ce daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci wurin taro da Hameed Ali a Seme da ke jihar Legas akwai jakadan Najeriya a kasar Benin; Kayode Oguntuase, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS); Mohammed Babandede, shugaban tawagar jami’an tsaro da ke aiki a kan iyakokin Najeriya; birgediya janar E. A Ndagi da sauransu.

Shugaban hukumar NIS ya ce ana fake wa da damar shigo wa da kaya cikin Najeriya wajen aikata abubuwan da basu dace ba, tare da bayyana cewa an rufe iyakokin domin masu ruwa da tsaki su shiga taitayinsu, su fara biyayya da mutunta dokokin kasa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.