Mahaifi ya kulle ‘yar shekara 16 tsawon shekara 2 saboda kin amincewa da auren dole

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un

Mahaifi ya kulle ‘yar shekara 16 tsawon shekara 2 saboda kin amincewa da auren dole

Jami’an Hukumar Kula da Laifin Fataucin Mutane, NAPTIP ta kama wani mutum dan shekara 62 mai suna Muhammad Ujujud saboda garkuwa da kuma kulle wata yarinya ‘yar shekaru 16, Fatima, tsawo shekaru biyu.

Ujudud, mazaunin kauyen Rinji a karamar hukumar Madobi ta jihar Kano, ya azabtar da yarinyar saboda kin karbar mijin da ya tilasta mata ta aura.

Mahaifin ya kulle Binta da dan uwanta, Shehu a cikin wani daki na daban a cikin gidansa.

Wakilin majiyarmu ya habarto cewa dan uwan ya mutu a tsare a kwanan nan.

Wani dan asalin yankin da ya tona ashirin mutumin ga manema labarai ya bayyana cewa mutumin ya shahara wajen aiwatar da hukuncin da ya shafi danginsa kuma ana jin tsoron sa a ƙauyen.

NAPTIP sun kai Binta wani asibiti mai zaman kansa a Kano, a yanzu haka tana karbar magani.

Kwamandan hukumar ta NAPTIP, Shehu Umar, ya tabbatar da kama Ujudud, yana mai cewa a yanzu haka ana ci gaba da bincike.

#LifeInArewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.