An Gano Wani Gida Da Aka Garkame Yara Dari Uku A Ciki A Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun bankado wani gida a cikin garin Kaduna da aka tara yara masu kananan shekaru da masu matsakaitan shekaru wasun su kuma daure da mari.

An gano wannan gida ne a unguwar Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi.

Daga cikinsu akwai kananan yara da basu wuce shekaru goma ba, inda yaran suka tabbatar da cewa ana yin luwadi da su.

Haka zalika kananan yara sun fallasa cewa ana tilasta musu yin azumi ba a son ransu ba, saidai an yi sa’a kwamishinan ‘yan sandan jahar, Ali Janga ya isa wajen, kuma sun dauke yaran daga gidan, sa’annan za su kaddamar da bincike.

Majiyar Taskar Labaru ta ruwaito cewa an samu wasu yara masu matsakaicin shekaru da aka same su da mari a kafafuwansu, sai dai mutanen da suka tara yaran a gidan sun bayyana cewa gidan horo ne, ma’ana suna horas da kangararrun yara ne.

Wata majiya daga rundunar ‘yan sandan tace wasu daga cikin daliban sun taho ne daga kasashen Burkina Faso, Mali da wasu jahohin kasashen Afirka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: