‘Yan Gudun Hijira Sun Rufe Hanyar Legas Zuwa Kaduna A Garin Kagara

Daga Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

Matsalar tsaro na cigaba da ta’azzara a Jihar Neja, inda barayi ke cin karen su ba babbaka a kauyukan, Kukoki, Wayam, Hana Wanka da sauran kauyukan dake kananan hukumomin Shiroro da Rafi.

Sakamakon kamarin da matsalar tayi yasa mazauna kauyukan suka yi gudun hijira zuwa garuruwan Kagara, Pandogari da Zungeru domin tsira da rayukan su, sun kuma zargi gwamnati da kasawa wurin daukar matakin da yadace, inda sukace a kowani lokaci barayin na zuwa kauyukan nasu suna kashesu tare da sace dukiyoyin su da yiwa mata fyade, amma babu wani kwakkwaran mataki da gwamnati ta dauka a kai hakan yasa suka yanke shawarar barin kauyukan nasu domin shigowa gari.

Wani mazaunin garin na Kagara daya daga cikin garuruwan da ‘yan gudun hijirar suka yada zango da ya bukaci a sakaya sunan sa saboda dalilai na tsaro ya shaidawa wakilin mu cewar ” Yanzu haka ‘yan gudun hijirar sun cika garin Kagara mazan su da mata da kananan yara, wanda yakai a jiya suka gudanar da gagarumin zanga zangar da takai ga rufe babban hanyar Legas zuwa Kaduna inda suke yin kira ga gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta daukar mataki akan matsalar domin barayin sun riga sun mamaye kauyukan nasu, sun hana su kwanciyar hankali balle suyi noma da kiwo da suka saba.

‘Yan gudun hijirar dake cikin dake cikin mawuyacin hali sun samu tallafi daga hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Neja inda aka raba masu abinci da kayan bukatar yau da kullum.

Tuni gwamnatin Jihar Neja tayi Allah waddai da wannan al’amari inda gwamnan Jihar ta Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yayi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar duk wani mataki da yadace domin kawo karshen wannan matsalar, ya kumayi kira ga rundunar soja da ta kaddamar da wani cibiya na horar da jami’anta a wannan daji da barayin ke cin karen su ba babbaka wanda hakan zai taimaka wurin kakkabe barayin a cikin katafaren dajin.

Mazauna kauyukan da masharhanta lamuran tsaro su danganta kazantar wannan matsalar da kwararowar barayin da suka ki mika wuya a shirin sasancin da gwamnatin Jihar Zamfara takeyi da barayin.

Koma da meye dai mun jira muga matakin da gwamnati da jami’an tsaro zasu dauka da kuma irin sakamakon da zai bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: