Shari’ar Buhari da Atiku: PDP za ta garzaya Kotun Koli, ta ce akwai rashin gaskiya cikin wannan hukunci

 

Jam’iyyar PDP ta bayyana rashin amincewarta da hukuncin da kotun zaben Shugaban kasa ta yanke a ranar Laraba, inda ta ce babu komi cikin hukuncin face rashin adalci ne da kuma salon karan tsaye ga dimokuradiyyar Najeriya.

 

Jam’iyyar ta PDP ta ce abinda yayi matukar ba ta mamaki game da shari’ar shi ne yadda kotun ta shafawa idonta toka ta ki yanke hukuncin gaskiya. Duk da cewa hujjoji da dama sun bayyana gabanta wadanda ke nuna rashin sahihancin zaben Shugaba Buhari.

 

A wani zance da kakakin jam’iyyar PDP ya fitar, Kola Ologbondiyan ya ce: “Wannan abinda takaici ne da mamaki a ce kotu na goyon bayan rashin gaskiya kiri-kiri a fili duk da tarin hujjojin da suka bayyana a gabanta game da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari.”

 

Jam’iyyar ta kara da cewa, kotun tayi amfani da wani abu wanda yake a fili a boye ba ta hanyar kin sauraron jawabin shaidu daga bangaren dake kara. A cewar PDP kawai dai anyi rufa-rufa ne kana aka ce ai shari’a ta zo karshe kuma Buhari shi ne yayi nasara.

 

“ ’Yan Najeriya da dama sauran kasahen duniya na ganin abinda ya faru, ta yadda kotu tayi kutun-kutun a kan maganar takardar WAEC na Buhari bayan da shaidu sun tabbatar bai mallaki takardar ba. Amma sai ga shi kotu ta gaskata cewa ya mallaki takardar.” Inji PDP.

 

A karshe jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga magoya bayanta da kuma sauran al’umman Najeriya na su kwantar da hankalinsu kuma ka da su kariya domin za su daukaka kara zuwa kotun koli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.