Jami’an Tsaro Sun Kama Mawaki Naziru Sarkin Waka

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

A cikin daren larabar da ta gabata ne bayan sallar Isha’i jami’an tsaron farin kaya suka dira gidan mawaki Naziru M Ahmad, Wanda aka fi sani da Naziru Sarkin waka in da suka yi binceke a gidan kafin daga baya suka tafi da shi ofishin su domin cigaba da bincike.

Majiyar mu ta kusa da mawakin ta shaida mana cewar da suka je gidan sun yi bincike a Studio na mawakin da yake cikin gidan nasa dake unguwar Karkasara a cikin garin Kano, kafin daga baya su tafi da shi ofishin su.

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan labarin babu tabbacin dalilin da ya sa aka kama mawakin, amma dai mutane suna ganin yin wannan kamun ba ya rasa nasaba da siyasa, duk da dai Shugaban Hukumar Tace Fina-Finan Isma’il Afakallah, ya ce kamun bashi da alaka da Siyasa.

Kuma yana kan hanya da zaran ya tsaya zai kira wakilinmu domin Rarrabe Zare da Abawa.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda lamarin zai kaya nan gaba.

#Insidearewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.