An kama Madugun masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja da Kaduna Na Hallaka mutane da Dama 

Rundunar ‘yan sandan IRT da mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari ke jan ragamarta tayi nasarar kame wani da ake zargi da zamowa madugun ‘yan garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

 

Wanda ake zargin Bello Adamu mai lakabi da Yalo ya shirya yin garkuwa da mutane sama da sau 50 akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, tare da halaka mutane da dama, ya ce yana kashe mutane ne idan ‘yan uwansu sun zage shi ta wayar salula, ko kuma idan sun yi jinkirin biyan kudi inda suke dan jinkirtawa.

 

Ya ce, yaran sa na kashe mutum idan ‘yan uwansa sun yi jinkiri sai yaransa su kashe mutum lamarin da ya alakanta da kaddara ko karar kwana.

 

Bello Yalo, ya ce ya karbi kudin fansa a lokuta da dama da suka kai daga Naira miliyan 3 har zuwa Naira miliyan 20, ya ce zuwa yanzu ya saci shanu sama da dubu 100 kuma suna nan ya garke su.

 

Allah Kawowa Mana Karshen wannan masifa A Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.