‘YAN MATA A KULA KADA GARIN NEMAN GIRA A RASA IDO

Ana yin kunshin henna ga mata domin kwalliya da ado amma abun yana neman zama musiba.

Wannan Yarinyar da alama ta samu tabon da sai dai mutuwa saboda sinadarin henna da ta yi amfani da shi bai yi daidai da yanayin jikinta ba.

Kasancewar sinadarin kemikal mai suna para-phenylenediamine (PPD) dake cikin lallen henna yana karawa lallen ba’ki da kuma dadewa bai wanke ba, amma kuma yana bada illa a jiki matukar jikin bai aminta da shi ba.

‘Yan mata a yi hankali ko kuma a koma ma lalle na gargajiya da muka sani da gishirin kunshi, shekara da shekaru iyayen mu suna amfani da shi bai cutar da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.