BAYAN SULHU: ‘Yan Ta’adda Sun Soma Sako Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Su A Katsina


A ci gaba da shirin sasanci da sulhu da Gwamnatin jahar Katsina take yi da masu kai hare haren ta’addanci a wasu sassa na wannan jihar, a jiya an mika mutane guda bakwai da suke tsare a hannun jami’an tsaro wadanda ba a riga aka yanke wa hukunci ba.

Ta bangaren su kuma, a shekaranjiya sun dawo da mutane biyar, (mata uku maza biyu). A jiya kuma sun sako mata guda goma da yarinya ta goye guda daya, dukkan su kuma mutanen garin Shinfida ne ta karamar hukumar Jibia.

Ana kuma jiran su sako sauran mata takwas da yara guda goma.

Ya Allah Ka dafa mana, wannan shiri yayi nasara mu sami zaman lafiya mai dorewa a wannan jiha tamu mai albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.