Ta Bankawa Kanta Wuta, Saboda Saurayinta Bayada Kudin Aurenta

Wata yarinya maisuna Aisha anguwar albarkarwa dake nan garin gusau ta yaiyafawa kanta fetur ta kestawa kanta ashana. Wannan alamari ya farune jiya assabar, a anguwar albarkawa gusau.

A zantawarmu da mai unguwar anguwar alh Aminu Muhammad ya shaida mana cewar lokacin da abun yafaru yarinyar tafito waje tana kururuwa na Neman agaji a waje yayin dasu matasa suka yi kanta tareda kashe mata wutar da tuni taci zarafinta.

Yayin zantawarmu da Aisha ta bayyana mana cewar ta dauki wannan mataki ne sanadiyar saurayin nata bashida kuddin auren ta kuma iyayensa basu hali ita kuma saboda zumudi irin na soyyaya taga da ta aikata zina gara ta kashe kanta duk dayake tasan kisan kai babban laifine.

Yanzun haka dai wannan boyar ALLAH tana nan kwance rai kwa-kwai mutu kwa-kwai a gidansu sanadiyar rashin kudin zuwa assibiti. Kamar yadda mai unguwar shiyar ya shaidawa manema labaru ko da abun yafaru ₦ 750 kacal ne agidan don haka ba zarafin zuwa assibit.

Da wannan ake neman masu tausayi kuma masu hali dasu ceto rayuwar malama Aisha
Dafatar ALLAH yakaremu da aikata aikin dana sani.

#InsideArewa

Leave a Reply

Your email address will not be published.