An Zabi Garin Nabardo Domin Aiwatar Da Binciken Kimiyar Noma Na Jancao A Jihar Bauchi

Bayan halartar babban taron kasa da kasa da Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya yi a kasar Amurka akan binciken kimiya da ya shafi noma. Inda aka kaddamar da sabon bincike akan abincin dabbobi da samar da makamashi na a duniya mai suna (Jancao).Bayan gudanar da wannan bincike gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar, ta zabi garin Nabardo a karamar hukumar Toro domin aiwatar da wannan bincike da jami’an Fujian na aikin gona da rainun yayan itatuwa na kasar China tun a shekarar 2016 na ciyawan (Jancao)Mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi akan sadarwa Alh Shamsuddeen Lukman Abubakar, ya bayyana hakan a shafin sa na sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.