Yadda Mu Ke Buga Takardun Kammala Digiri Na Bogi A Kan Naira Dubu Biyu Kacal, Cewar ‘Yan Cuwa-Cuwa

Daga Aliyu Muhammed Auwal

Wasu ‘yan cuwa-cuwa da harkallar ‘business centre’ da aka kama a Maiduguri, sun bayyana wa jami’an tsaro yadda suke buga satifiket din digiri a kan naira dubu biyu kacal.

Jami’an NSCDC ne suka gabatar da su a yau Talata a bisa zargin su da aikata fojare na satifiket din jabu a shagunan da suke harkokin kwamfuta da intanet a Maiduguri, babban birnin Jihar Barno.

Hukumar ta ce ta na binciken wadanda ake zargin su takwas da laifin buga Satifiket na jabu, takardun shaidar dauka ko shiga jami’a, ‘ID cards’, rasidan biyan kuin makaranta da tambarin sitamfi na jami’o’i da daman a Arewacin kasar nan, ciki har da Jami’ar Maiduguri.

An gabatar da wadanda ake zargin tare da wasu daga cikin satifiket da takardun rasidan jabun da suka buga. An kamo su ne daga kasuwar hada-hadar buga takardu da ke bakin Gidan Waya (Post Offfice), a Maiduguri.

Babban Kwamandan NSCDC na Jihar Barno, Abdullahi Ibrahim ne ya gabatar da su, tare da cewa “jami’an sa sun shafe watanni takwas su na binciken wannan badakala.”

Daga nan sai Ibrahim ya danganta dalilin da ya sa ake samun yawaitar irin wadannan takardun jabu da cewa saboda duk aikin da matashi zai yi, sai a ce ya kawo takardar shaida.

Ya ce yawancin takardun duk na masu neman aiki ne da kuma masu neman gabatar da takardun shaidar rashin lafiya ko wani ciwon da suka ce ya na damun su.

Sannan kuma ya kara da cewa sun gano akwai hannun wasu ma’aikatan wasu jami’o’i a cikin harkallar.

Daya daga cikin wadanda kae zargin, wanda ya ce shi ma’aikacin Jami’ar Maiduguri ne, wato Abubakar Abubakar, ya ce abokin sa ne ya jefa shi a cikin wannan harkallar.

Ya ce har naira 2000 ko 1000 su na karba idan za su yi satifiket na digiri ko kuma katin shaidar wurin aiki, wato ‘ID card.’

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.