Ta Kashe Sabon Mijinta, Domin Ta Koma Gidan Tsohon Miji

Matar wadda ta Hada Kai tare da wasu maza Biyu Garba Hassan Da Sahabi Garba Suna Zaune ne a Sabon Gari dake karkashin Gundumar Illo dake karamar Hukumar Bagudu a Jahar Kebbi.

Matar dai ta Kashe mijin nata Mai Suna Abdullahi Shaho ne domin ta Auri Tsohon Mijinta Mai Suna Idris Garba kamar Yanda Shugaban ‘Yan Sandar Jihar Kebbi Muhammad DanJuma Ya Fada.

Shugaban ‘yan Sandar Muhammad DanJuma Yace, Za’a Gurfanar da matar da Mazan Biyu a gaban kotu domin su fuskanci Hukuncin abinda suka aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.