Wata Sabuwa Kuma: Kotu Ta Yi Watsi Da Daukaka Karar Da Atiku Yayi

 

Kotun koli ta soke wani kara da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na Shugaban kasa a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abuakar suka shigar.

An shigar da karar mai lamba SC/738/2019 akan hukuncin kotun zaben Shugaban kasa, wanda a ciki ta yanke cewa Atiku da PDP ba su bayar da amsa ga wani kara da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar a ranar 14 ga watan Mayu.

Inda ta nemi a kori kalubalantar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Atiku da PDP ke yi a zaben Shugaban kasa da ya gabata.

A wani hukunci a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Datijo Mohammed, ya soke karar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.