‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 4 A Garin Tsayau Da Ke Karamar Hukumar Jibia A Jihar Katsina

Kwana Daya Da Tafiyar Shugaban Kasa Buhari:


…mun Yi kokarin kiran Jami’an tsaro domin su kawo Mana dauki, ba su zo ba

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Da marecen yau ne, wasu yan bindiga dauke da makamai, suka kai hari a kauyen Tsayau, da ke gundumar Mallamawa cikin Karamar Hukumar Jibia, inda suka kashe mutane hudu kuma suka sace masu shanu.

Da yake hira da manema labarai, daya daga cikin Matasan da suka kawo gawarwakin, a fadar Mai Martaba sarkin Katsina da ke Kofar Soro, Dogo Mande ya ce da misalin karfe ukku ne Yan bindiga su shidda dauke da manyan bindigogi suka shigo garin mu na Tsayau. Suka sace Mana shanu, muka bi su domin kwato shanun mu, nan muka Yi bata-kashi da su, suka kashe Mana mutane hudu har lahira.

Mande ya ci gaba da cewa wadanda suka hallaka dukkan su matasa ne akwai Buhari Musa, Surajo Lawal, Abdukarim Rabe da Kuma Kabir Yahya. Mun Yi kokarin sanar da jamian tsaro, da muka wulginsu suna shawagi. Ni da kaina na je na sanar da sojojin da ke suntiri kusa da garinmu na Tsayau, domin su kawo Mana dauki babu jamiin tsaron da ya zo. Hatta gawarwakin mutanen da suka kashe, sai dai sojojin jamhuriyar Nijar suka taimaka Mana.

Da yake bayyana dalilin zuwan su fadar Mai Martaba sarkin Katsina, ya ce mun gabatar da korafin mu a Mataki na Maigari, Hakimi da Kuma Karamar Hukumar Kan yadda yan bindigar ke kashe mu, ba wani Mataki da suka dauka. Shi yasa muka taho da su fadar Mai Martaba domin sanar da shi halin da muke ciki, domin a dauki matakin magance wanna matsalar. Mun fuskanci kalubale daga wajen jamian tsaro akan hanyar mu ta zuwa Katsina, muka jajirce muka ce sai mun zo.

Daga karshe dai an sanar da su Mai Martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya Yi tafiya Kuma sun juya da gawarwakin zuwa Tsayau, domin Yi masu sutura, da misalin karfe takwas da rabi na daren yau lahadi. An tabbatar masu da Mai Martaba ya dawo zaa kirawo su domin Jin korafin su.

Idan dai zaa iya tunawa jiya Shugaban Kasa Buhari ya Kammala hutun babban Sallah, inda ya bada Umurnin ga sojojin da suka karshe kashen kashen Yan bindigar da suka addabi Kananan Hukumomin Batsari, Safana, Danmusa, Jibia, Faskari da Kuma Sabuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.