Ya Yi Batar Dabo Bayan Ya Watsawa Matarsa Da ‘Ya’yanta Ruwan Guba

Wani magidanci a garin Dandume dake jihar Katsina ya yi batar dabo bayan ya yi wa matarsa mai suna Rabi da ‘ya’yanta uku wanka da ruwan guba a yayin da suke kan bacci da dare.

Rahotani sun bayyana cewa mijin wanda har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a gan shi ba, ma’aikaci ne a bankin Union dake garin Funtua.

Wani abin mamaki kuma shine, lamarin wanda ya auku kimanin mako guda da ya gabata, har yanzu babu wani dauki da Rabi da ‘ya’yanta suka samu daga hukuma balle a kai su asibiti neman magani, inda suke ci gaba da zama a haka a gida sakamakon rashin kudin da za a garzaya da su asibitin Ahmadu Bello kamar yadda aka gaya musu a babban asibitin Funtua.

Suna matukar neman agaji kama daga kula da lafiyar su da kuma kwatar musu hakkinsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.