Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Adamawa, a ranar Laraba, ta ba da sanarwar tsawaita makonni biyu na wa’adin jam’iyyun siyasa don kammala zaben fitar da gwani na ‘yan takarar da zasu fafatawa a zaben kana nan Hukumomi a watan Nuwamba a jihar.
Shugaban hukumar Alhaji Isa Shettima ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Yola.
Shettima ya ce kawo yanzu an sanya ranar 21 ga watan Satumba, maimakon ranar 31 ga watan Agusta da aka sa a Baya.
Ya yi bayanin cewa canjin ya samo asali ne sakamakon Hutun Bukukuwan Babbar Sallah.
Shugaban ya ce duk ranakun da aka tsara don wasu ayyukan kamar yadda yake kunshe cikin jadawalin zaben da aka bayar tun da farko bai canza ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, ya zuwa yanzu, African Democratic Congress ADC, All Progressives Congress APC, Peoples Democratic Party PDP da Social Democratic Party SDP, sun nuna sha’awar shiga zaben kuma tun lokacin da aka fara sayar da fom ga masu neman takara.