HAJJIN BANA: Nijeriya Ta Sha Ruwan Addu’o’i A Wurin Shugabanninta Da Malamanta

…tsayuwar Arfa na bana ya gudana lami lafiya

Daga Ibrahim Baba Suleiman

A yammacin Asabar din nan manyan Malamai da manyan kasa suka hadu a filin Arfa suka yi addu’oi na musamman ga kasar Nijeriya, wajen samun zaman lafiya mai dorewa ga kasa, habaka tattalin arziki tare da hadin kai ga ‘yan kasar a dukkan bangarori.

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, shi ya jagoranci addu’ar ina sauran Malamai suka rufa masa baya. Sheikh Abdurrazak Hausawiy, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Yakubu Musa Hassan, Sheikh Kabiru Gombe, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, Sheikh Nasiru Abdul’Muhyi, Sheikh Farfesa Okene, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, Sheikh Gwani Alkhadi, da Sheikh Injiniya Aliyu Burga na daya daga cikin Maluman da suka halarci Addu’oin.

A bangaren shugabanni kuwa Akwai shugaban majalisar Dattawa Alh. Ahmed Lawan, da Sanatoci wadanda suka rufa masa baya, da yan majlisun majalisar wakilai, Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Kauran Bauchi, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni duk sun samu halarta.

Alhaji Aminu Dantata, Alhaji Dahiru Mangal, Alhaji Muhammad Babandede (Magajin Rafin Hadejia), Sanata Ahmad Sani Yeriman Bakura, Sanata Abdul Ningi da sauran daruruwan mutane suka halarci addu’oin wacce ta gudana karkashin jagorancin Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, tare da kulawar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau.

Allah ya amsa mana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.