Hadarin Mota, Ya Lakume Rayuka 11 A Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara.

Wakilinmu Shuaibu Ibrahim Gusau

Da yammacin yau asabar ne mutane goma sha daya suka rasa rayukansu sakamakon mummunan hadarin mota da ya auku a kusa da garin Damba dake karamar hukumar gusau a jihar zamfara.

hadarin dai ya farune da wata mota kirar sharon inda ta shige cikin babbar mota kirar DAF.

Kamar yadda aka bayyana shi mai sharun din ya tasone daga Abuja zuwa shinkafi domin hidamar sallah Inda ya ke cikin mugun gudu ya shige cikin babbar motar.

Gwamnan jihar zamfara. Hon Bello muhammad Matawallen Maradun, ya ziyarci inda akayi hadarin kuma ya bada umurnin daukar gawarwakin zuwa garuruwansu, tare kuma da bada umurnin tallafawa iyalan mamatan karkashin jagorancin Hon. J. Ahmad dan Majalisa mai wakiltar shinkafi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.