Gwamna Ganduje Zai Gina Kwalejin Koyar Da Ayyukan Fasaha Ta Mata Zalla

 

A yunƙurinsa na ƙarfafa wa ƴaƴa mata gwiwa kan neman Ilimi da sana’o’in dogaro da kai a wannan zamani, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya amince da gina sabuwar Kwalejin koyar da ayyukan fasaha ta ƴaƴa mata zallah domin tunkarar ƙalubalen da ke fuskantar su a rayuwa.

“Mu na buƙatar matan mu su yi gogayya da sauran mata wajen samun ingantaccen cigaba. Mu na buƙatar su kasance daga cikin fannin cigabanmu. Tare da ra’ayin samar musu ƙarin dama domin su ba da tasu gudunmawar wajen bunƙasa da cigaban Jiharmu da ƙasa baki ɗaya”. Cewar Gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a jiya a ya yin da ya karɓi baƙuncin shugabannin kwalejin Ilimi ta Jihar Kano tare da al’ummar fannin karatun sharar fage waɗanda su ka ziyarce shi a Ofishinsa ƙarƙashin jagorancin shugaban makarantar, Dakta Sunusi Yakubu Ahmad.

“Imaninmu kan ilimin ƴaƴa mata zai kai su mataki nagaba. Shi ya sa mu ka sanar da aniyarmu ta samar da kwalejin koyon Ilimin ayyukan fasaha ta mata zallah”. Inji gwamna Ganduje.

“A duk lokacin da aka yi maganar Ilimi, abin da ke fara zuwa raina shi ne gina rayuwar ɗan adam. Sannan mun yanke shawarar daga Kwalejin zuwa mataki nagaba, kamar yadda mu ka yi wa sauran makarantu”. Inji Gwamna.

“Ilimi ba tare da tsari ba, ba a cimma nasara, wannan dalili ne ya sanya a ko da yaushe mu ke tsara fannin Iliminmu domin ya ginu cikin nasara. Dukkan nasarorin da shugaban makarantar ya faɗa waɗanda ku ka cimma a fannoni da dama, ba mamaki za su iya samuwa saboda mun yi tsari a fannin Iliminmu.

Kuma gwamna Ganduje ya yi alƙawarin kammalawa makarantar ginin ɗakin karatu na zamani domin ingantuwar Ilimi a tsakanin ɗalibai da malamai.

Gami da alkawarin fitar da ɗalibin makarantar wanda ya samu lalurar rashin gani ƙasar waje domin duba lafiyarsa.

Ya yin da ya ke nasa jawabin, Shugaban makarantar Dakta Sunusi, ya yabawa gwamna Ganduje kan irin haɗin-kai da goyon bayan da ya ke ba su wajen ciyar da harkar Ilimi gaba.

Inda ya ke cewa “mai girma gwamna wannan makaranta ta cimma nasarori masu yawa waɗanda babu su kafin yau. Mu na godiya mai girma gwamna. Inji Dakta Sunusi.

Daga ƙarshe kuma ya miƙa wa mai girma gwamna lambar yabo ta girmamawa wacce asusun kula da manyan makarantu na ƙasa (TETFUND) ya ba shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.