Cunkoson Motoci : Gwamna El-rufai Ya Yi Tafiyar Kilomita 13 A Kafa Don Taimakawa Matafiya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed Elrufai, da kansa yake taimakama matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. Inda ya yi tafiya a kasa ta kusan kilomita 13 sannan kuma ya kwashe fiye da awanni uku akan hanyar don ganin matafiya sun samu saukin dogon layin ababen hawa wanda ya fara tun yammacin jiya sakamakon rufe hanyar da wasu direbobi suka yi bayan wani jami’in tsaro ya kashe abokin aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.