Masu Kashe Gobara Sun Ceto Rayuwar Wasu Mutane Uku A Kano

Hukumar kashe gobara a jihar Kano a jiya Lahadi sun bayyana cewa jami’ansu sun yi nasarar ‘yanto rayuwar mutum uku a wani kwantaccen ruwa a Kano.

Kakakin hukumar Alhaji Saidu Mohammed shi ne ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kano. Yace sun ‘yanto wadannan mutum uku din ne da yammacin ranar Lahadi a BUK road a Dan’agundi dake Kano Municipal.

Wadanda suka ‘yanto din sun hada da; Mohammed Hamza, 22, Sadiq Sunusi, 17, da Ibrahim Gambo, 21. Ya ce tuni suka mika wadanda suka ‘yanto zuwa ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike. Ya gargadi al’umma da su sanya ido sosai musamman a lokacin daminar nan, sannan su guji yin wanka a budadden wuri ko kwantaccen ruwa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: