A kokarin sa na inganta harkokin tattalin arziki a jihar, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya haramta bangar siyasa a fadin jihar baki daya.
Gwamnan ya bayyana haramcin ne lokacin da yake kaddamar wani shirin gwamnatin sa na samarwa matasa aikin yi wanda ya gudana a Filin kwalon kafa na Elkanemi, wanda anan take matasa 2,762 suka anfana da shirin, inda kuma yayi alkawarin cewa nanda watanni shida zai samarwa matasa 4000 aikin yi, karkashin shirin samarwa matasa aikin yi mai suna (BOYES) a takaice.
Zulum ya gargadi Matasa da cewar duk wanda aka kama yana bangar siyasa a fadin jahar to yayi kuka da kasa.
Zulum ya kuma bayyana bangar siyasa a matsayin wata annoba da ka iya wargaza tattalin arzikin kasa da kuma lalata tarbiya.
Wannan haramcin na cikin daya daga cikin alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zaben sa.