Boko Haram Sun Kashe Masu Jana’iza 65 A Borno

 

Irin barnar da mayakan Boko Haram suka yi a garin Budu bayan harin da suka kai
Hukumomi a Najeriya sun ce adadin mutanen da suka mutu a harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Badu-Abattari na jihar Borno, ya tashi zuwa akalla 65.

Bayanai sun nuna cewa da misalin karfe 10 na safiyar ranar Asabar ne ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne a kan babura suka yi dirar mikiya a kan wasu mutane da ke kan hanyarsu ta dawowa daga makabarta bayan yin sutura, yankin Nganzai da ke gefen birnin Maiduguri.

‘Yan kungiyar sun bude wa mutanen da ke dawowa daga garin Badu Kuluwa da ke kusa da Goni Abachari wuta irin ta kan mai uwa da wabi, inda su ka kashe mutum 65.

‘Yan sintiri ne suka dauko gawarwakin mamatan bayan da wadanda suka samu suka tsira sun sanar da su.

Maharan Boko Haram dai na yawan kai hare-hare yankin na Nganzai, inda ko a watan Satumbar da ya gabata sai da ‘yan kungiyar suka yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Nganzai, Muhammed Bulama, ya shaidawa manema labarai cewa yawancin mutanen sun mutu ne lokacin da suka farwa maharan:

“Sun kai musu hari ne a makabarta lokacin da suka je binne wani mamaci. Kuma nan take suka kashe mutum ashirin da daya. Daga bisani lokacin da sauran jama’a suka ji labari, sai suka bi maharan domin su far musu, amma sai ‘yan Boko Haram din suka sake kashe su. Hakan ne ya sa adadin ya kai 65.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin yana mai cewa ya samu tabbaci daga jami’an tsaron kasar cewa ‘yan ta’addar da suka kai harin za su dandana kudarsu.

Har wa yau, ‘yan Boko Haram din sun yi awon gaba da shanu da sauran nau’in dabbo daga kauyuka guda biyu da ke yankin na Nganzai a watan Satumba.

Fiye da mutum miliyan biyu ke gudun hijra saboda rikicin Boko Haram.

Rahotanni na cewa da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ma sai da ‘yan Boko Haram din suka kai farmaki wani sansanin ‘yan gudun hijra da kone wani sansanin sojoji da ke wajen birnin na Maiduguri duk a kokarin satar abinci.

A ranar Talatar nan ne dai rikicin na Boko Haram ke cika shekara 10 cif-cif da fara shi, tun bayan kashe shugaban kungiyar Jama’atu Ahlussunnah Lidda’awati Wal Jihad da aka si sani da Boko Haram, Muhammad Yusuf, a ranar 30 ga watan Yulin 2009.

Rikicin Boko Haram ya fadada zuwa kasashe masu makwabtaka da Najeriya kamar Chadi da Niger da Cameroon, inda kididdiga ta ce an yi asarar rayuka kusan 30,000 sannan fiye da mutum miliyan biyu sun bar matsugunansu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: