Ba Shi’a Za Mu Haramta Ba:~Buhari

 

Garba Shehu a hirarsa da BBC Hausa ya ce; za ku iya yin ayyukan Shi’a (amma banda gwagwarmaya).

Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa za a aiwatar da wannan hukunci na kotu domin haramta kungiyar ta IMN, amma ya ce hakan ba yana nufin haramta Shi’a ba.

“Akwai miliyoyin ‘yan Shi’a a kasar nan wadanda suke zaune lafiya kuma gwamnati ba ta da matsala da su, ba wanda zai tsangwama musu kan yadda suke harkokinsu, Ba mu hana kowa yin Shi’arsa ba,” In ji Malam Garba.

Ko ya Mabiya Shi’a Musamman Almajiran Sheikh Zakzaky za su Kalli wannan Batun na Malam Garba Shehu, Wani Dan Shi’a Mai Suna Isma’il Balarabe, cewa yayi ai dama ba Buhari ne ya Bamu dama muke yin Addini ba Balle ya hanamu.

Isma’il, ya Kara da cewa Wannan Zancen na Buhari, ya fi kama da tabarmar Kunya wacce Hausawa ke cewa da Hauka ake nadeta domin ta ya wanda baka sashi ba za ka hanashi?

Kuma in dai kisa ne yau suka fara ko yau za su daina, mu fa ku daina Babatu akan hanawa ko rashin hanawa kawai ku cigaba da aikin da kuka dauko mu ma zamu cigaba da yin namu amma muna muku albishir saura kiris ku kawo karshen kanku da kanku, inji shi

Me za ku ce?

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: