Za A Saka Hannu Kan Yarjejeniyar Bunkasa Wutar Lantarki A Nijeriya

 

A yau Litinin ake sa ran za a rabbata hannun yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Nijeriya da Kamfanin Siemens na kasar Jamus akan ayyukan samar da hasken lantarki mai inganci a Nijeriya.

Kamfanin Siemens sun kware wajen samar da hasken lantarki a Duniya, domin cikin kasa da shekara biyu kacal suka samar da hasken lantarki mai karfin 10,000mw a kasar Egypt…

Sanya hannun da za a yi, ya biyo bayan ganawar da shugaba Buhari ya yi da shugabar kasar Jamus Angela Merkel a shekarar da ta wuce, inda yanzu haka shugaban Kamfanin Siemens Joe Kaeser yana Nijeriya don saka hannu akan fara aikin inganta hasken lantarki a Nijeriya.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.