‘Yan Shi’a Sun Kashe Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda A Lokacin Zanga-Zanga

Wani mataimakin kwamishan ‘yan sanda mai kula da ayyuka a rundunar ‘yan sandan birnin Abuja, Umar Usman, ya rasa ransa a ranar Litinin, lokacin da aka yi artabu tsakanin rundunar ‘yan sanda da ‘yan shi’an da ke zanga-zanga a birnin Abuja.

A dangane da rahoton PRNigeria, masu zanga-zangar sun hallaka Umar a lokacin da ‘yan sandan ke kokarin hana su lalata kayayyaki a kusa da sakatariyar gwamnatin tarayya.

Daily Nigerian ta yi rahoton cewa zanga-zangar ta koma tashin hankali a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan shi’an ne suka kone ofishin hukumar da ke kula da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), wanda yake a kusa da sakatariyar gwamnatin tarayya, Abuja.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: