Gwamna Ganduje, Ya Kaddamar Da Kwamitin Aikin Yin Ruga, Ya Kuma Gayyaci Makiyayan Jihar Kano

 

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da Kwamitin nazari akan kirkiro da Mazaunun makiyaya da ake kira Ruga da masana’antun Madara, mai mambobi 16.

Yace za a gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar bankin Ciyar da Islama gaba.

Da yake kaddamar da kwamitin, a fadar gwamnatin jihar Kano, Ganduje yace idan aka samar da matsugunen makiyayan zasu amfani al’umma ba ma na jihar Kano kadai ba, har ma da ‘yan wasu jihohin da ma makiyayan sauran kasashen yammacin Afrika Baki daya.

Ya kara da cewa kwamitin na da muhimmacin gaske bisa la’akari da amfanin Ruga da ake hangowa da kuma Cigaban da hakan zai haifar na Bunkasar Tattalin Arziki a jihar.

Dukkan mu mun san da irin matsalar da ake fuskanta sakamakon rashin matsugunen makiyaya a kasar nan, inji Ganduje.

Yace makiyaya kala uku ne, akwai wadan da suke karakarar su suna kiwo a kusa da gidajen su, wannan basa tada fitina, akwai masu yawo daga arewa zuwa kudancin kasar nan a lokutan rani don neman abinci da ruwan da za su ba Shanun su sa’annan su koma mazaunan su.

Dan haka Muna Kira ga wannan Kwamiti da Babban Murya da su yi aiki Tukuru wajen Sauke nauyin da aka Dora musu domin fitar da abin da zai zama Mafita a jihar, inji shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.