Kotu Ta Bada Belin Wadda Ta Yi Yunkurin Kashe Mijinta A Kano

 

Babbar kotun jihar Kano mai lamba daya ta bayar da belin Fatima Hamza da aka fi sani da Hanan, wacce ake zargi da yunkurin kashe mijin ta Said Hussein bayan da ta caka masa wuka.

Jagorar kungiyar Mata lauyoyi ta kasa FIDA Barista ta shaidawa kotun cewar tuhumar da ‘yan sanda suka yi wa Hanan ba ta da tushe domin fada suka yi ya bangashe mata hakora ita kuma ta soka masa wuka, suka yi kare jini biri jini.

Barista Lamido Abba Soron Dinki dake zaman lauyan gwamnati bai yi suka ba, dan haka kotu ta bayar da Hanan beli nan take.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.