Wata Matashiya A Bauchi Ta Jefa Jaririyar Da Ta Haifa A Rijiya

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi ta sanar da kama wasu matasan mata guda biyu saboda jefar da jariran da suka haifa ba tare da aure ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar, ya shaidawa manema labarai ranar Litinin cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wata matashiya, Hauwa Ishaku, mai shekaru 23, wacce ta haihu a cikin wani kango sannan ta jefa jaririn a cikin wata toshuwar rijiya.

Hauwa, ‘yar asalin kauyen Bidir a yankin karamar hukumar Azare, ta jefa jaririn ne a cikin wata tsohuwar rijiya da babu ruwa a cikin ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun gaggauta zuwa wurin bayan an sanar da su abinda matashiyar ta aikata. Ya ce jami’an sun yi nasarar samun jaririn da ran sa, kuma sun dauke shi zuwa asibitin tarayya na garin Azare domin a duba lafiyarsa, sannan sun kama Hauwa.

DSP Abubakar ya kara da cewa, Hauwa ta sanar da rundunar ‘yan sanda cewa ta jefar da jaririn ne saboda tsohon mijinta da ya yi mata ciki ya ki amincewa da ita sannan kuma ba ta da halin da zata iya daukar nauyin kan ta balle na jaririn da ta haifa.

Ya kara da cewa yanzu haka Hauwa da jaririn na hannun hukumar walwala ta jihar Bauci.

Kazalika, kakakin rundunar ya sanar da cewa sun kama wata matashiya, Aisha Bashir, mai shekaru 17, da ke zaune a unguwar Hotoro Danmarke a jihar Kano, wacce ta zo har jihar domin ta jefar da jaririn da ta haifa mai sati uku kacal a duniya.

Matashiyar ta jefar da jaririn ne a kofar gidan wani mutum mai suna Kabiru Abubakar da ke unguwar Kaji a garin Azare.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce jami’an ‘yan sanda sun garzaya zuwa wurin tare da tserar da jaririn bayan sun samu rahoto.

Abubakar ya kara da cewa sun kama har mahaifiyar matashiyar.

A cewaer kakakin, matashiyar ta ce ta yanke shawarar jefar da jaririn ne bayan iyayenta sun juya mata baya tare da jaririn da ta haifa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.