Jam’iyar PDP ta gabatar da kakakin kungiyar kamfe din Atiku, Alhaji Buba Galadima, a matsayin sheda a gaban kotun saurarar kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja.
Jam’iyar PDP da dan takararta na kujerar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, na kalubalantar sakamakon zaben 23 ga watan Fabrairu wanda aka bayyana Muhammadu Buhari na jam’iyar APC a matsayin wanda ya samu nasara.