An Kai Jami’in Hukumar Kwastam Asibiti Sakamakon Zargin Tabin Hankali


An kwantar da wani jami’in hukumar kwastam mai matsayin ‘Assistant Superinyendent’, a asibiti sakamakon nuna wasu alamu na tabin hankali a shelkwatar hukumar, ranar Litinin.

Kakakin hukumar kwastam, Joseph Attah, ya bayyana cewa jami’in kwastam din mai suna Nura Dalhatu ya je aiki a shelkwatar hukumar kwastam din da ke Abuja, ranar Litinin.

Attah ya ce an yi wa nura wasu tanbayoyi, inda shi kuma ya bayar da amsoshin cikin wata siga da ke nuna kansa ba daya ba.

Ya kara da fadin cewa tuni aka dauki jami’in zuwa asibiti domin a duba lafiyarsa tare da yi masa magani. Ya shawarci ‘yan Nijeriya da su tausaya wa halin da yake ciki tare da yi masa addu’ar Allah ya bashi lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.